Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fallasa cewar ba bambancin addini ko ?abilanci ne matsalar ?asar ba, mutanen ?asar ne matsalarta da kansu.
Buhari ya fa?i hakan ne a lokacin da ya kar?i ba?uncin ?an ?ungiyar Muhammadu Buhari/Osinbajo (MBO) Dynamic Support Group, da ke goyon bayan shugaban da mataimakinsa, a ranar Laraba.
A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin ya?a labarai Femi Adesina ya fitar, Buhari ya ce “kanmu za mu zarga idan aka zo batun halin da Najeriya ke ciki, saboda irin rashin adalcinmu.”
Sanarwar ta ce ?an ?ungiyar sun kai wa Buhari ziyara ne don gabatar masa da kundin irin nasarorin da aka samu a tsawon shekara biyar na mulkinsa.
A yayin da shugaban ke ganawa da ?an ?ungiyar, ya yi waiwaye kan irin fadi tashin da ya shafe shekaru yana yi don ganin an yi masa adalci a za?ukan da yake da ya?inin ya yi nasara a cikinsu.
Ya bayar da misali da cewa a za?ukan 2003 da 2007 da kuma na 2011, duk mutanen da suka ?i yi masa adalci ?an ?abilarsa ne kuma addininsu ?aya.
Yayin da wa?anda suka tsaya masa kai da fata kuma suka kasance ?an wata ?abilar daban kuma addininsu ba ?aya da shi ba.
“Matsalarmu ba ?abilanci ko addini ba ne, mu ne matsalar kanmu,” in ji shugaban.
