Zulum Ya Bukaci A Janye Karin Kudin Makaranta Da Aka Yi A Jami’ar Maiduguri

Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya yi kira ga shugabannin jami’ar Maiduguri da ke jihar da su janye sabon karin kudin karatu da suka yi. Rahoton ya nuna Mai girma Babagana Umara Zulum ya yi wannan kira ne domin a tausayawa marasa karfi da ke karatu.

Sannan Farfesa Babagana Zulum yana ganin idan aka rage kudin makarantar, hakan zai saukakawa wadanda rikicin yakin Boko Haram ya auka masu. Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin da wasu daga cikin shugabannin jami’o’in jihar suka kai masa ziyarar sallah a gidan Gwamnati a Maiduguri.

Mataimakin shugaban UNIMAID, Farfesa Mohammed Laminu Mele da Farfesa Umaru Kyari Sandade na jami’ar Jiha ne suka ziyarci Gwamnan a fadar gwamnati dake birnin na Maiduguri. Rahoton ya ce a nan ne Gwamna Zulum ya yi amfani da wannan dama wajen kokawa cewa iyaye da-dama sun cire ‘ya ‘yansu daga jami’ar tarayyar.

Farfesa Zulum yake cewa mutum fiye da 500 suka kawo masa kuka domin a rage kudin. “Ina mai matukar sane da kalubalen da jami’a ta ke fuskanta, amma ko N500, 000 za ku ka rika samu daga kowane dalibi, ba za a shawo kan su ba. Na samu kiraye-kiraye fiye da 500 a kan karin kudin makarantar da aka yi. Ina so in tsoma baki, ina so shugaban jami’a ya ji kukan mutanen Borno.”

Related posts

Leave a Comment