Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar za?a??en Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zauna da wasu daga cikin masu neman kujerar shugabancin majalisar dattawa a majalisa ta goma da za a rantsar a watan Yuni.
Rahoton ya tabbatar da zababben shugaban na Najeriya ya hadu da manyan Sanatoci irinsu Godswill Akpabio da Barau Jibrin a gidansa. Ba za a iya cewa ga wainar da aka toya a wajen wannan zama da aka yi a yammacin Talata a Abuja ba, amma da alama ba zai wuce neman kamun kafa ba.
Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu da shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila su na cikin wadanda aka zauna da su. Rahoton ya nuna akwai Gwamnonin jihohin Ogun da Ekiti da su Sanata Olamilekan Adeola, Sanata Opeyemi Bamidele da kuma Sanata Emmanuel Bwacha a cikin zaman.
Sanatan Legas ta gabas, Tokunbo Abiru, mataimakin shugaban APC, Abubakar Kyari da James Faleke su na cikin mutanen da aka kebe da su a gidan Tinubu. Wata majiya ta shaida cewa makasudin zaman shi ne a fito da yadda za ayi rabon kujerun majalisar tarayya tsakanin bangarorin Kudu da na Arewacin kasar.
