Zulum Ne Silar Nasarar Da Muke Samu A Yaki Da Boko Haram – Rundunar Soji

Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Kwamandan runduna ta 7 na hukumar sojojin Najeriya, Manjo Janar, A.A. Eyitayo, ya bayyana cewa ba tare da roko ba, Zulum ya tallafawa sojoji a lokuta da dama.

Kwamandan ya yi wannan furucin ne yayin da gwamnan ya kai ziyara hedkwatar sojojin dake Maiduguri ranar Lahadi.

Rahotanni sun bayyana cewa Zulum ya halarci taro na musamman da sojojin suka shirya domin taya GOC murnar ?arin girman da ya samu zuwa Manjo Janar.

Kwamandan sojojin yace: “A lokuta da dama ba tare da mun zo nema ba, ka kawo mana ?auki da taimakon kayayyaki.” “Ta hanyar cikakken goyon baya da taimakon ka (Zulum), sojoji na ?ara samun kwarin guiwa wajen ?ara kaimi a fagen yaki.”

Daga nan kuma, GOC din ya roki Zulum ya isar da sakon yabo da jinjinar sojoji ga shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, da hafsan sojin ?asa, bisa zakulo sojojin da suka cancanta da ?ara musu girma.

Related posts

Leave a Comment