Zargin Satar Kudi: Yahaya Bello Ya Kori Kwamishina

Rahotanni daga Jihar Kogi na bayyana cewar Gwamna Yahaya Bello na jihar ya sauke Dr Saka Haruna Audu daga mukaminsa na kwamishinan lafiya na jihar kuma matakin ya fara aiki nan take.

A cewar majiyoyi, an tsige kwamishinan ne kan zargin karkatar da wasu kudade, Wata majiya ta ce Dr Saka ya tattara kayansa daga ofishinsa da ke ma’aikatar lafiya ta jihar da ke garin Lokoja, babbar birnin jihar a ranar Talata.

An tattaro cewa wasu mutane na ta rokon gwamnan kan cewa kada ya bayyana lamarin ga duniya ta sani.

An kuma ruwaito cewa Dr Saka ya sanar da wasu takwarorinsa cewa an dakatar da shi ne, amma ba a kore shi ba.

Related posts

Leave a Comment