Zanga-Zangar A Kori Fulani Ta ?arke A Edo

Bayan guguwar fitina ta kyamatar Fulani da ta ?arke a yankunan Jihohin Yarbawa dake Kudu maso yammacin ?asar nan, dubban Mata ne suka fito suka cika manyan titunan dake Benin City babban birnin Jihar Edo suna kiran a gaggauta korar Fulani daga jihar.

Matan sun bayyana cewa yanzu basu iya zuwa gonakinsu domin noma, basa iya fita kasuwanci sannan ‘ya’yan su ba sa samun zuwa Makarantu sakamakon ayyukan ta’addanci da Fulani ke aikatawa a yankin na kisa da garkuwa da Mutane a kusan kullum suna kar?ar kudin fansa.

Masu Zanga-Zangar sun yi kira da babbar murya gwamnati da ta gaggauta korar Fulani Makiyaya daga jihar, domin samun natsuwa gami da zaman lafiya da kuma samun kariya daga fitinar Fulanin, Matan sun tare hanyoyi hanyoyi a babban birnin jihar gaba ?aya.

Dubban Matan suna rike da wasu takardu masu rubutun #FulanimustGo, matan sun ce zuwa gonakinsu ya gagara saboda suna tsoron kada makiyaya su kashesu.

A bangare guda, kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bayyanawa al’ummar Fulani dake kudancin Najeriya su dawo gida idan ana koransu daga inda suka zaune.

Hakazalika Kungiyar Dattawan Arewa ta yi kira ga gwamnonin Arewa su shirya karban Fulanin dake shirin dawowa gida daga kudu.

Related posts

Leave a Comment