Gwannatin Tarayyar Nijeriya ?arkashin jagorancin mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ta nuna damuwarta kan yiyuwar samun karancin man fetur a ?asar.
Karamin Ministan man Fetur Timipre Sylva ya bayyana haka a lokacin wani taro tsakanina Gwannatin da kungiyoyin kwadago a daren Litinin.
Taron dai ci gaba ne a tattunawar da bangarorin ke yi a kokarin da ake na shawo kan kungiyoyin kwadagon kar su tafi yajin aiki biyo bayan karin farashin man da wutar lantarki.
A lokacin zaman taron kwamitin aiki kan karin farashin man ya gabatar da rahotonsa yayin da na wutar lantarki ya ce har yanzu yana kan aikin hada nasa Rahoton.
Bayan taron ne Sylva ya yi garga?in cewa bada wasu sati uku don yin nazari kan rohoton da aka gabatar zai iya shafar wadatuwar man a kasuwa.
