Zan Goyi Bayan Tinubu A Zaben 2023: Tanko Yakasai

?aya daga cikin dattawan arewacin Najeriya Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa zai goyi bayan tsohon gwamnan jihar Legas Bola Ahmed Tinubu a yun?urin da Tinubun yake na neman shugabancin Najeriya.

A wata hira da jaridar Punch, Tanko Yakasai ya shaida cewa Tinubu ya zo wajensa ne a ranar Laraba domin ya nemi goyon bayansa.

Duk da cewa Tinubu bai fito fili ya bayyana cewa zai yi takarar shugabancin ?asa ba, amma akwai rahotanni da dama da ake ya?awa cewa zai tsaya takarar.

Haka ma akwai hotuna da kuma manyan allunan kan hanya ?auke da hoton Tinubu a wasu sassa na Najeriya da ke nuna alamun zai tsaya takarar shugabancin Najeriya.

Related posts

Leave a Comment