Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewa ?an takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sha alwashin ceto jihar daga hannun yan ta’adda, wa?an da suka kashe, garkuwa da raba dubbanin mutane da gidajen su, idan ya zama shugaban kasa.
Atiku ya ?auki wannan al?awarin ranar Laraba da daddare bayan gana wa da ?an takarar gwamnan Zamfara karkashin PDP, Dauda Lawal Dare.
An ruwaito Atiku Abubakar na cewa mutanen Zamfara na gab da tsira daga halin da suka tsinci kan su. Tsohon mataimakin shugaban kasan ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da sakaci har matsalar ta ya?u, yanayin da a cewarsa ya maida jihar koma baya da talakawanta.
A wata sanarwa da hadimin ?an takarar gwamnan Zamfara ya fitar, Atiku ya ce matakin farko na ceto jihar shi ne mutane su maka APC da ?asa a za?e. Atiku ya ce: “Idan muna son cimma nasara dole mu ha?a kai a PDP hakan zai bamu cikakken damar fuskantar abokan hamayya duk rintsi duk wuya.”
“Babban abinda mazauna Zamfara ke so a musu shi ne a dawo da zaman lafiya, a tsare gonaki da kuma samar da kasuwanci. Amma yanayin yanzu ba haka yake ba, wajibi mu kawar da APC don ceto da gina jiha da kasa baki ?aya.”
