Zan ?arasa Rayuwata A Daura Idan Na Bar Mulki – Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya ce zai koma mahaifarsa wato Daura ta jihar Katsina da zarar ya sauka daga mulki a shekarar 2023.

Domin ya samu hutu, da kuma nesanta kansa daga matsaloli idan ya sauka daga mulkin ?asar ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Rahotonni sun ambato shugaban na fa?in haka ranar Lahadi lokacin da ya kar?i ba?uncin mazauna babban birnin ?asar, wa?anda suka kai masa ziyarar gaisuwar Kirsimeti a fadarsa.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana godiyarsa ga ‘yan ?asar saboda yarda, da goyon baya da kuma damar da suka ba shi na jagorantarsu.

A lokacin ganawar Buhari ya tabbatar wa masu ziyarar cewa zai fi samun kwanciyar hankali a Daura.

A wani labarin na daban Shugaba Buhari ya bayyana cewa a tsawon mulkin sa ya yi kokarin ganin Najeriya ta zama abar gwaji ga wasu kasashe da kuma gyara kasa, amma har yanzu wasu sun saka shi a gama sun tsangwamar sa

Buhari ya fa?i haka a wurin taron bikin taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

” Na yi imani ina iya bakin kokarina amma duk da haka, iyawata ba ta isa ba, wasu ?an Najeriya na tsangwamata.

” Na ?osa wa’adin mulki na ya xika in koma gida can Daura in maida hankali kan gonata ka-in-da-na-in. Amma kafin wannan lokacin zan ci gaba da aiki tukuru a matsayina na shugaban kasa domin tabbatar an samu ci gaba mai ?orewa kamar yadda muka sa a gaba

Mutanen Najeriya na gani a wannan ?arnin ba a ta?a shugaban kasa da ya samu irin goyon bayan da ?an Najeriya suka bashi ba kamar shugaba Muhammadu Buhari.

Buhari ya kafa tarihin kada shugaban kasa mai ci a 2015. Sai dai kuma musamman a zangon sa ta biyu, mutanen Najeriya da dama na ganin ba abinda suke tunanin Buhari zai yi wa ?an Najeriya ne ya ke yi ba.

Misalai da masu hasashe sukan yi kan ha?a da irin matsalolin rashin tsaro da ya addabi musamman yankin Arewa da kuma tsadar kayan abinci da masarufi.

Sannan kuma ga matsalolin tashin man fetur da tsadar rayuwa wanda kafin ya zu an yi tunanin Buhari zai kawo karshen ireiren wadannan matsaloli ne.

Related posts

Leave a Comment