Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kwamishina a hukumar jin dadin yan sanda PSC, Naja’atu Mohammed, ta bayyana cewa kudaden da ma’aikatan gwamnati suka sace a ?ar?ashin mulkin Buhari cikin shekaru 8 da suka shude ba kadan bane.
A cewarta, da za’a rabawa kowane ?an Najeriya wadannan kudade, kowa zai samu N732,000 la?adan ba tare da ?ata wani lokaci ba.
Ta bayyana hakan ne a hirar da tayi da gidan Rediyon Freedom FM, Kano yayin taron gabatar da lambar yabo ga wani jami’in dan sanda, Daniel Iste Amah wanda ya nuna gaskiya da ri?on amana akan aikin sa.
Jami’in dan sandan da shugaba Buhari ya karrama kan kwatanta gaskiya da tsoron Allah inda ya ki karban cin hancin $200,000 daga wajen wani barawo a Afrilun 2022.
Hajiya Naja’atu ta bayyana cewa idan ba a dakile wannan satan da ake yi ba, nan da 2030 kudin da za’a sata zai kai a rabawa kowani dan Najeriya N1.4m.
“Daga 2014 kawo yanzu, kudin da aka sata a Najeriya na da yawa. Da za’a rabawa kowane dan kasar, har da jaririn da aka haifa yau, sai kowa ya samu N732,000.” “Bisa bincike, idan kuma aka cigaba da hakan har nan da 2030, abun zai munana. Idan za’a dawo da dukkan kudin da aka sata a lokacin, sai kowa ya samu N1.4million matsayin rabonsa.”
