Zamfara: APC Ta Yi Asarar Manyan Jiga-Jiganta Biyu

Rahotanni daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Alhaji Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Garba marafa sun sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.

Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP a jihar, Ritaya kanal Bala Mande, ne ya sanar da hakan jim kadan bayan gama wani taron masu ruwa da tsaki a Gusau, babbar birnin jihar a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu.

Mande ya bayyana cewa sun zauna sannan sun yanke shawara kan batun sauya shekar Yari da Marafa sannan sun cimma yarjejeniyar aiki don ci gaban jam’iyyar.

“Duk mun yarda za mu yi aiki don ci gaban jam’iyyar sannan PDP a jihar ta yi maraba da su a cikinta. Za mu tabbatar da gaskiya da adalci ga dukka mambobinmu har bayan mun lashe zabe a 2023.

“Za a sanar da ranar gagarumin bikin dawowarsu jam’iyyamu daga bisani amma za mu aiwatar da dukkan yarjejeniyar da muka cimma a yayin taron masu ruwa da tsaki.”

Sakataren labaran bangaren Yari na APC, Alhaji Ibrahim Muhammad Birnin Magaji, ya tabbatar da ci gaban amma bai yi karin bayani ba. “Eh, da gaske ne za mu koma jam’iyyar adawa ta PDP, kuma iya abun da zan iya fadi kenan a yanzu.”

Related posts

Leave a Comment