Rahotanni daga Jihar Anambra na bayyana cewar har kawo ya zuwa yanzu ana cigaba da tattara sakamakon zaben Gwamna da ya gudana a ranar jiya Asabar.
Wani mai sanya ido na hukumar za?e ta ?asa INEC ya shaida wa BBC cewa ya ga wakilan jam’iyyu daban-daban a rumfunan za?e na siyan kuri’ar jama’a a wasu yankunan jihar, da suka ha?ar da karamar hukumar Dunukofia, da Anaocha, da Awka, da Njikoka da Aguata.
Jami’in ya ce ”Jama’a kin fitowa suka yi sai wajen ?arfe hu?u na yamma, saboda an fara fito da ku?i, an fitar da kudi sosai, kowacce jam’iyya ma ta siya, su kansu wakilan jam’iyyun sun rinka sasantawa a tsakaninsu, idan wakilin wata jam’iyya a wata rumfa ya ga baza su kai labari ba sai ya sasanta da wanda yake da rinjaye a wannan wajen.”
Ya ?ara da cewa ”Ni da idona na ga ana siyar da ?uri’a a kan Naira dubu uku, wasu wuraren naira dubu biyar, su jami’an tsaro saboda sun ga za?en na gudana cikin lumana sai suka mayar da hankalinsu zuwa tsakiyar jihar, ya kasance wasu wuraren ma idan ka je baza ka tarar da ko jami’in ?an sanda daya ba.
Jami’in ya ?ara da cewa za?en ya gudana cikin lumana, don duk rumfar ka?a ?uri’ar da ka je za ka taras da mutane suna annushuwa suna farin ciki babu wata alamar fargaba, saboda kwanciyar hankalin da aka samu
”Tun da nake halartar za?e ban taba ganin inda aka jibge jami’an tsaro kamar wannan ba, shi yasa ma ?an ?ungiyar IPOB suka janye matakin da suka ?auka na hana za?en, domin sun lura cewa idan ma suka yi wani yun?uri ba za su kai labari ba” inji shi
To sai dai ya ce ”An samu matsala da na’urorin za?e, a wurare da yawa bayan an shirya an kammala komai ga kayan za?e amma na’urori suka ki tantance masu jefa ?uri’a sai wajen yamma aka fara”.
A halin da ake ciki dai ana jiran ganin wanda zai lashe za?en, wanda yan takara goma sha takwas daga jam’iyyu daban-daban suka fafata.
