Za Mu Shawo Kan Matsalar Tsaro Nan Da ‘Yan Makwanni – Hukumomin Tsaro

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa hukumomin tsaro sun sha alwashin nan da makwanni masu zuwa za su fara aiki kan wasu sabbin dabaru don magance matsalar tsaro da tashe-tashen hankulan da ke faruwa.

Hukumomin tsaron sun yi wa shugaban ?asa alkawarin cewa za a samu sauyi a ?o?arinsu duk da cewa akwai wani ?an cikas ta ?angaren tsare-tsare da za su iya fuskanta.
“Kuma sun fahimci girman irin hakkin da ke wuyansu,”

Mai bai wa shugaban ?asar shawara kan tsaro Janar Monguno mai ritaya ya kuma ce majalisar ta tattauna kan matakin da aka kai wajen bincike kan harin da ?ungiyar ISWAP ta kai wa gidan yarin Kuje a farkon watan nan, wani al’amari da ya girgiza kowa a duk fa?in ?asar.

“Manufar ita ce fitowa da wasu shawarwari kan matakin da za a ?auka kan wa?anda ke alhakin faruwar wannan abin, da kuma tabbatar da irin hakan ba ta sake faruwa ba har abada a ?asar nan.”

Sai dai kuma ya ce majalisar ?oli ta harkokin tsaron ta damu da irin yadda kafafen watsa labarai ke bayar da rahotannin tashe-tashen hankulan da ?asar ke fuskanta.

Kazalika ba ta jin da?in irin kalaman da ke fitowa daga bakunan wasu shugabannin siyasa da ake ganin kimarsu a ?asar.

Ya ce “bugu da ?ari kuma, majalisar ta kuma da mu game da irin rahotannin da kafafen watsa labarai ke bayar wa game da rashin tsaro.

Related posts

Leave a Comment