Buhari Bai Da Masaniyar Barazanar ‘Yan Bindiga A Kanshi – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya ce shi ne ya sanar da shugaban kasa Buhari game da barazanar da ‘yan bindiga suka yi cewa za su kama shugaban da shi gwamnan.

Gwamman ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da ‘yan jarida da ake yada wa kai tsaye, a ranar Laraba da daddare.

Idan dai ba a manta ba a karshen makon da ya gabata ne ‘yan bindiga masu ikirarin jahadi suka fitar da wani biidiyo da ke nuna mutanen da suka sace na jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, tun a watan Maris inda a ciki suke barazanar cewa sai sun kamo shugaban kasar da gwamnan.

El-Rufai ya ce shi Buhari bai ma san da wannan barazana ba sai da ya gaya masa, sannan kuma Gwamman Jihar Zamfara Bello Matawalle ya kaiwa shugaban hoton bidiyon ya gani.

Gwamnan ya ce ai shi daman tun baya da shekara biyar yake bayar da shawara da a shiga dajin a yi wa sansanoninsu ruwan bama-bamai, da cewa ta hakan ne za a yi maganinsu.

Related posts

Leave a Comment