Shugaban Sojojin Nijeriya, Janar Yusuf Buratai ya bayyana cewa, za su kunyata kungiyar Boko Haram da ISWAP a cikin shekarar 2021.
Ya bayar da wannan tabbaci ne a wajan murnan sabuwar shekarar 2021 da aka yi a mahaifarsa dake Biu a jihar Borno.
Ya ce sojojin Nijeriya sun yi kokari matuka a shekarar 2020 wajen yaki da ‘yan ta’adda inda ya ce sun kuma dukufa domin sun ga bayan ‘yan ta’addar a fading Nijeriya.
Kalaman Janar Buratai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ganin rashin katabus na rundunar Sojin kasar duba da yadda Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda ke cigaba da cin karen su babu babbaka.
A jawabin da Shugaban ?asa ya gabatar wa ‘yan Najeriya na sabuwar shekara, Buhari ya bada tabbaci ga ‘yan Najeriya na cewar za’a kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi ?asar nan bada jimawa ba.
