Gamayyar ?ungiyoyin fararen hula a ranar Juma’a sun ce za su bijire wa shirin ?ara farashin man fetur da ake zargin ?ungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu (IPMAN) na ?o?arin yi.
A wata sanarwa ta ha?in gwiwa da Dr Basil Musa da Mallam Haruna Maigida suka fitar na cewa za su bijirewa yun?urin IPMAN, na ?ara farashin litar man fetur zuwa N700 ta hanyar rufe gidajen man IPMAN da ke fa?in Najeriya.
?ungiyoyin dai sun ha?ar da Oil and Gas Transparency and Advocacy Group da Civil Society Coalition for Economic Development (CED), da Centre for Citizens Rights da Centre for Good Governance Advocacy da kuma Action against Corruption in Nigeria, da sauransu.
Sun dai zargi IPMAN da zama kishiyar gwamnati da ?ara tsanani a kan talakawan Najeriya, ta hanyar ?arin farashin man fetur su ka?ai.
