Hukumar Sa-ido da Hana Sauti Gur?ata Yanayi (NESREA) ta bayyana cewa ta na da ?arfin ikon gurfanar da duk wani coci-coci, masallatai da masana’antu masu yin abin da ya kira “damun jamai da ?arar da ta wuce ?a’ida’ maka su kotu domin a hukunta su.
Babban Daraktan NESREA, Aliyu Jsuro ne ya bayyana haka a wata ganawar da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ranar Lahadi a Abuja.
Aliyu ya bayyana cewa jama’a da dama na kai ?orafe-?orafen yadda wasu wuraren ibadu da masana’antu da gidajen ka?e-kade ke damun su da ?ara.
Sai ya ce bai kamata ana ?ure ?arar lasifika a wuraren ibada ko ka?e-ka?e ba, saboda ana shiga ha??in mutane, tsirrai da dabbobi.
“Idan ?ara ta yi yawa, ta na yi wa tsirrai, dabbobi da mutane illa.
“Matsawar ana cika wa mutum kunnuwa da ?ara, to lafiyar za ta tawaya har ya samu hawan jini da wasu cututtuka.”
Ya ?ara da cewa shi ya sa hukumar su ke bi su na wayar da kan jama’a dangane da muhimmancin rage ?arar na’urori irin su lasifika da sauran mu.
“Za mu ci gaba da bi ana wayar wa masu wadannan wurare kai. Mu kan aika da takardun garga?i sau biyu. Na uku kuwa dama kawai gurfanarwa ce a kotu.” Inji shi.
Idan ba a manta ba, a cikin watan Yuni ?in nan ?asar Saudiyya ta sa dokar hana kunna lasifika a masallatan ?asar fiye da 30% bisa 100 % na ?arar lasifika ?in.
