Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa, Abin mamaki ne yanda mutane suke tsayawa basu baiwa kansu kariya idan an kai musu hari, yace hakan sam bai dace ba.
Ya bayyana hakane a Hedikwatar ‘yansandan jihar Katsina inda ya kadamar da cibiyar sadarwa da zata taimaka a yaki matsalar tsaro.
Yace jama’ar jihar Katsina ba zasu iya dogaro da jami’an tsaro kadai ba wajan samun tsaro. Gwamnan yace ba zaka tsaya a kauyen ka saidai kawai ka kira waya idan an kawo hari ba, ba tare da daukar kowane mataki ba
Yace suma ‘yan Bindigar mutanene kamar kowa amma suna da bindiga, yace yanzu babu wata dabara da mutane zasu iya samawa kansu akan ‘yan Bindigar?
