Sokoto: An Shiga Makokin Rasuwar Magajin Gari

Rahotanni daga Sokoto birnin Shehu na bayyana cewar al”umma sun shiga makoki tun bayan bayyanar rasuwar magajin garin Sokoto kuma jikan Sardaunan Sokoto Alhaji Hassan ?anbaba A Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa Magajin Garin Sokoto, Alhaji Hassan Danbaba kuma Shugaban masu nada sarki na masarautar Sokoto, ya yanke jiki ya fadi ne a otel dinsa a Kaduna misalin karfe 11.30 na safiyar ranar Asabar.

Ya rasu a hanyarsa ta zuwa asibiti a Kaduna, wani na kusa da iyalansa, Alhaji Buhari Sarkin Tudun Jabo, ya tabbatar da rasuwar a Kaduna bayan gajeruwar rashin lafiya.

Rahotanni sun bayyana cewa Magajin Garin na Sokoto ya zo Kaduna ne ranar Alhamis domin ya jajantawa tsohon Ministan Tsaro, Janar Aliyu Gusau, bisa rasuwar dan uwansa. “Kamar yadda ya saba, ya sauka a otel dinsa, Stonehedge a birnin Kaduna.

“Gusau da Magajin sun yi shirin su bar Kaduna tare su tafi Abuja a ranar Asabar. Bayan ya yi wanka misalin karfe 11 na safe ya saka kaya domin ya tafi wurin Janar Gusau a gidansa.

Ana shirin tafiya, ya yanke jiki ya fadi. Hadimansa suka taru suka dauke shi suka kama hanyar asibiti nan take. Amma, a hanya sai ya ce ga garinku.

Magajin Garin na cikin manyan yan Najeriya da suka hadu a Legas a makon da ya gabata domin tattaunawa kan yadda za a kawo karshen matsalolin Najeriya gabanin 2023.

Related posts

Leave a Comment