Yunwa Na Dab Da Zama Annoba A Najeriya – Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, gargadin da ofishin kula da Noma da abinci na majalisar Dinkin Duniya yayi cewa akwai yiyuwar shiga matsananciyar Yunwa a Arewa bai kamata a yi watsi dashi ba.

Ya bayyana cewa wanan gargadi kamata yayi ya zaburar da gwamnatin tarayya ta dauki mataki, musamman lura da cewa, Arewa ce ke samar da Abinci a Najeriya.

Yace idan Arewa ta samu matsalar Abinci, zai taba gaba dayan Najeriya dama kasashe makwabta.

Atiku yace matakin da Gwamnati ta dauka na tsame hannunta dsga harkar Abinci bai kamata ba kuma ya kamata ta canja Tunani.

Atiku yace matsalar Abinci, matsala c da zata iya kawo matsalar tsaro a Najeriya dama makwabta idan ba’a magance ta da wuri ba.

Atiku ya bayar da shawarar yanda za’a magance matsalar inda yace babbar matsalar itace manoma da yawa da masu sana’ar kayan gona basa iya zuwa gonakinsu saboda matsalar tsaro.

Yace yana noma sosai kuma yana da ma’aikata akalla 10,000 dake masa aiki dan haka yana da masaniya akan lamarin.

Atiku ya kuma bayyana cewa, abinda yake bayar da shawara shine a kafa wata rundunar jami’an tsaro ta musamman da za’a tura yankunan da manoma ke noma an basu tsaro.

Yace kuma gwamnati ta karawa manoma lokacin biyan basukan data basu, yace babu yanda za’a yi mutum bai yi noma ba ace ana son ya biya bashin da aka bashi.

Related posts

Leave a Comment