Zamfara: Matawalle Ya Yi Rantsuwar Barranta Daga ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya ce manyan masu fa?a aji da mutane da a ke ganin ?imarsu na daga cikin masu taimaka wa yan bindiga masu sace mutane a jihar.

Matawalle ya bayyana cewa akwai wasu kwararan hujjoji da ya dogara da su, wa?anda suka nuna mutanen na da hannu a lamarin dumu dumu wanda hakan babban abin takaici.

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Zailani Bappa, ya fitar, ya ce bisa dalilin haka ya sa mai girma gwamna ya rantse da Alkur’ani don tabbatar wa da kuma nesanta kan shi daga zargin hannu a lamarin.

Ya kuma bukaci sauran mambobin majalisar gwamnatinsa da su bi sahun shi, su rantse da Littafin Allah mai tsarki, Alkur’ani, domin nesanta kan su daga ayyukan yan ta’adda.

Bayan haka ya ?alubalanci baki ?aya Zamfarawa da yan siyasa da duk wasu masu fa?a aji su ?auki Al?ur’ani su rantse domin tsame kan su daga zargin ala?a da yan ta’adda.

“Wasu daga cikin wa?an nan mutane masu ?ima ne kuma jiga-jigai da ake ganin girman su (suna taimaka wa yan ta’adda), haka nan akwai masu amsar ku?a?e domin kwarmata wa yan bindiga bayanai.”

Gwamnan ya ce duk wa?an da ke cikin gwamnatinsa sun bi umarninsa sun Rantse, amma tsohon mataimaki, Mahdi Gusau, ya gaza bin matakin domin tsaftace kansa daga zargi. Gwamnan ya kara jaddada cewa gwamnatinsa ba zata gajiya ba har sai ta ga bayan yan bindiga duk da goyon bayan da suke samu daga wasu bara gurbi.

Related posts

Leave a Comment