‘Yan Najeriya Sun Yi Tir Da Karin Kudin Lantarki

IMG 20240225 WA0030

Tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da ?arin ku?in wutar lantarki ga masu samun wutar lantarki ta tsawon sa’o’i 20 a kullum wa?anda suke ajin A kenan, ‘yan kasar na ci gaba da nuna damuwa da korafe-korafe da kuma tambayoyi kan lamari.

Wannan matakin dai ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriyar ke kokawa kan mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki da kuma tsadar rayuwa.

A ranar Laraban da ta gabata ne hukumar da ke kula da wutar lantarkin a Najeriyar ta sanar da sabon farashin da abokan huldarsu za su fara biya.
Hukumar ta ce kwastomomi za su fara biyan naira 225 a kan kowane ma’auni daya na wutar (unit) inda a baya suke biyan N66.

‘Yan Najeriya da dama, wa?anda tuni suke fama da ?alubalen tsadar rayuwa, da hauhawar farashin kayan masarufi, ?arin kudin lantarkin ya kara dagula musu lissafi.

A shafukan sada zumunta kamar su X wato Twitter da Facebook, ‘yan Najeriya da dama sun bayyana ta?aicinsu da damuwarsu kan karin kudin wutar lantarkin.

Mun le?a wa?annan shafukan domin za?ulo wasu ra’ayoyin al’ummar Najeriya game da wannan ?arin kudin lantarkin.

Wani mai amfani da shafin X, Shehu Gazali Sadiq ya rubuta a shafin nasa cewa

“Sun cire tallafin man fetur ba tare da kafa wani kwamiti ba.

Sun kara kudin wutar lantarki ba tare da kafa kwamiti ba. Amma wajen ?ara mafi karancin albashi, sun kafa kwamitin da ba wanda ya san abin da suke yi. ’Yan siyasar Najeriya sun fi kowa zalunci a doron kasa.

Sharfuddeen Zubair Mahmoud, tsohon janar manaja na hukumar samar da wutar lantarki na Najeriya kuma darektan hukumar ba da lantarki ta Kaduna ne kuma ya yi wa BBC bayanin jerin azuzuwan wutar lantarki.

Mahmoud ya ce shekarun baya da dama mutanen Najeriya kan yi kuka kan rashin samun wuta duk da cewa suna biyan kudin lantarki, da wannan koken ne ya ce hukamar samar da wuta ta fahimci cewa akwai ?amshin gaskiya a koken nasu inda ya sa ta fitar da wannan sabon tsari.

A wannan tsarin ne Mahmoud ya ?ara da cewa hukumar ta zauna ta duba su waye ne ke samun wuta a rana, inda kuma aka gano cewa akwai wa?anda ke samun wutar har na tsawon awa 20 ko sama da haka ma.

Hakan ne ya sa hukumar ta ce dukkannin kamfanonin da ke samar da wutar lantarki su tabbatar cewa sun gyara ?angarorin da ke samun wutar lantarkin a kullum.

“A ta haka ne aka ce duk wa?anda ke samun lantarki na awa 20 a rana, su ne suka fa?a a ajin A, kuma su aka ?ara wa kudin lantarki.” in ji darektan.

” Akwai kuma ajin B wanda su kuma suna samun wuta ta tsawon sa’o’i 16 a kullum. Shi kuma ajin C kuma su ne ke samun wutar lantarki ta tsawon awa 12 a kullum.”

Ya ?ara da cewa “Akwai ajin D kuma su suna samun wutar lantarki ta tsawon awa 8 a rana

“Ajin E kuwa suna samun wutar lantarki ta tsawon awa 4 a rana.” in ji Mahmoud.

Ya ce farkon tsarin shi ne a cikin shekara biyu, ana sa burin tabbatar da cewa babu wanda a ?asar nan da ke samun wutar lantarki ?asa da awa 12.
Ta ya ya mutane za su gane ajin da suke?

Mahmoud ya ce yadda mutane za su gane ajin da suke shi ne duba shafukan intanet na dukkan kamfanonin da ke rarraba wutar lantarki a jihohi saboda duk za su buga, kuma tuni wasu suka buga sunayen dukannin unguwanni da wurare da azuzuwan da suke.

Ya kuma ce ita ma hukumar samar da wutar lantarki ta ?asa ta buga a nata shafin na intanet ta kuma ce nan gaba ka?an za ta saka a buga a jaridu da dama saboda mutane su fahimci ajin da suke.
Ga wa?anda ba su samu damar shiga shafin intanet ba, Mahmud ya ce za su iya tuntu?ar kwamitin da kamfanonin za su kafa inda za a tura bayanansu da lambobinsu ta sa?wannin wayar tarho.

“Na san ko wane kwastoma ya riga ya san ajin da yake tunda ba yanzu aka soma wannan abun na azuzuwa ba, kowane kwastoma ya san abin da yake biya.”

Ya ce duk wanda bai ga sunan uguwarsa ba a ajin A da aka buga a shafin intanet, to, ?arin farashin lantarkin bai shafe shi ba kuma ya ce akwai ?an ajin A da suka koma ajin baya saboda ba a biya musu bu?ata kamar yadda hukuma ta ce.

Daraktan ya ce ba zai yiwu wani da ke ajin E ya sami kansa yana biyan kudin lantarkin wa?anda ke ajin A ko na B ko na C ko na D ba.

Ya ?ara da cewa idan aka ce wata uguwa na cikin ajin A, duk kwastoman da ke wannan unguwar zai biya sabon farashin da aka fitar na lantarki.

Darektan ya kuma ce a tsarin da aka yi, ana son a cikin ko wanne wata shida akalla a dinga matsar da mutane gaba kamar a ce wanda suke ajin E na ?arshe a matsar da su zuwa ajin D ko ajin C duk bayan wata shida, wa?anda suke ajin A kuma a matsar da su zuwa ajin B, ko kuma ?an ajin B su koma zuwa ajin A ko ajin C duk bayan wata shida.

Ya ce idan kuma ‘yan ajin A ba sa samun wuta yadda ya kamata kamar a ce suna samu ta tsawon awa 4 ko 8, yayin da ya kamata su sami na awa 20, ya ce toh gaskiya da akwai miskila saboda haka za a mayar da su ajin da ke samun wuta a adadin wa?annan awowi..

Darekta ya ce wannan ?arin kawai ?an ajin A aka yi wa.

“Daman kudin lantarkin aji-aji ne, ba ku?in da ajin A ke biya ba ajin B za su biya ba.”

“Ajin B na biyan ?asa da abin da ajin A ke biya.Ajin C na biyan kudi ?asa da abin da ajin B ke biya. Ajin D na biyan kudin lantarki ?asa da abin da ajin C ke biya, hakazalika ma ajin E na biyan ku?i ?asa da abin da D ke biya.” in ji Mahmoud.
Ya kuma ce kudin lantarkin da ajin B zuwa E suke biya ya danganta da kamfononin rarraba lantarki saboda ku?in da suke sayar da lantarkin ya bambanta.

Mahmoud ya ce, “a wannan sabon tsarin, kowane kamfanin da ke rarraba hasken lantarki, hukuma ta saka shi dole ya kafa wani kwamiti na ko-ta-kwana na ma’aikatansa kuma za su fadi sunayensu tare da buga sunayen a shafin intanet dinsu da lambobinsu da komai.”

Darektan ya kara da cewa “sannan kuma za su aikawa duk wani kwastomominsu bayanan ta wayar tarho a matsayin sa?o cewa ga mutanen da suke mana aiki na ko-ta-kwana ko da suna da wani ?orafi ko kuma wata tangar?a da lantarkinsu ku yi musu magana.”

“Sanna kuma kowace rana, kwamitin za su ringa buga yawan hasken lantarkin da suka bayar da awowin da suka bayar a dukannin wa?annan wuraren.”

Related posts

Leave a Comment