Gwamnatin Legas Ta Kwace Baburan ‘Yan Arewa Masu Acaba 359

images (1)

Gwamnatin Jihar Legas ta sake ?wace baburan ‘yan aca?a har 359, wa?anda ke kabu-kabu a bakin mayanka dabbobi da kuma gefen titin jirgin ?asa.

Haka kuma an murtsike wuraren kwanan ‘yan share-wuri-zauna, domin a ?ara haskakawa da tsaftace wuraren.

Hukumar Tsaftace Legas daTilasta da Tirsasa Bin Dokoki ta bayyana haka a ranar Laraba, ta ce wuraren da aka ruguje duk bukkoki ne da masu kwana waje suka kakkafa saboda kunnen ?ashin kangare wa dokar hukuma.

Hukumar ta ce kuma an ?wace babura ne saboda ana zirga-zirgar ?aukar fasinja a daidai hanyar titin jirgin ?asa.

Kakakin rundunar kamen babura mai suna Gbadeyan Abdulraheem ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya aiko wa PREMIUM TIMES, ya ce an rushe ?akunan ne a Fagba.

Gagarimin aikin rusau da ?wace baburan sai ya ?auki kwanaki biyu ana gudanar da shi, bayan ?addamar da aikin titin jirgin ?asa a jihar.

Shugaban hukumar, Shola Jejeloye ne da kan sa ya jagoranci aikin rusau ?in a Fagba, Iju-Ishaga, Mayanka da Pen Cinema, inda aka ?wace babura masu ?imbin yawa.

Jejeloye ya ce ‘yan dabar da ke sagarabtu a mayanka sun ha?a kai da masu baburan su na hana jami’an su aikin ?wace baburan, amma duk da haka an yi nasarar ?wace babura 359.

Related posts

Leave a Comment