Na Azurta Sama Da Mutum 2000 A Jihar Kogi – Yahaya Bello

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce gwamnatinsa ta maida a?alla mutum 2,000 sun zama Miliyoniyoyi a jihar inda ta tsame su gaba daya daga talauci.

Ya yi wannan furucin ne a wurin taron ?ara wa juna sani game da manufofin sa a siyasar Najeriya karo na biyu wanda ke gudana a Abuja.

Yahaya Bello ya kuma bayyana shirinsa na za?ar mace ta farko a matsayin mataimakiyar shugaban ?asa idan APC ta lamunce masa ta bashi tutar takara a za?en 2023, kuma ta amince ya za?i wanda zasu tafi tare.

Yayin da yake amsa tambaya kan tsarinsa game da tattalin arzi?in kasar nan, wanda ya ha?a da al?awarin maida yan Najeriya miliyan 20 miliyoniyoyi zuwa 2030 idan ya gaji Buhari, gwamna Bello ya ce:

“Mun maida mutane mafi ?aranci mutum 2,000 sun zama Miliyoniyoyi a jihar Kogi.” Haka nan kuma game da wanda zai za?a su yi takara tare a matsayin mataimakin shugaban ?asa, Bello ya ?ara da cewa: “Idan aka bani damar na za?a da kaina, ba zan kauce wa tsagin jinsin mahaifiya ta ba. Zan so na tafi da mace ta farko a matsayin mataimakiyar shugaban ?asa a 2023.”

Related posts

Leave a Comment