Gwamnatin Benin ta saki jagoran masu fafutikar kafa kasar Yarbawa a Najeriya Sunday Ighoho.
An saki Ighoho domin ba shi damar zuwa ganin likita a asibiti bisa shara?in cewa ba zai bar asibiti ba ko Cotonou saboda wani dalili, kamar yadda ?aya daga cikin lauyoyinsa Yomi Aliyu, ya tabbatar wa manema labarai.
Ya ce Farfesa Wole Soyinka ?aya daga cikin shugabannin Yarbawa ya taimaka aka saki Sunday Ighoho domin zuwa asibiti.
A watan Yulin 2021 aka kama Sunday Ighoho mai da’awar kafa ?asar Yarbawa ta Oduduwa.
Ana tuhumarsa Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, da laifin shiga kasar ba bisa ka’ida ba tare da kokarin tayar da husuma, amma ya musanta hakan.
