‘Yan Najeriya Sun Daina Fallasa ?arayin Gwamnati – EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta ce ‘yan Najeriya sun yi sanyi da kwarmata bayanai kan masu satar kudin gwamnati duk da babban tukwicin da ke tattare da yin hakan.

Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya shaida hakan a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a birnin Kwara, wato Ilorin.

Shugaban ya ce akwai bukatar sake jan hankalin mutane da ankarar da su muhimmanci yin haka a kokarin kwato kudaden sata da sake gina tattalin arzikin kasa.

Sai dai hukumar ba ta yi karin haske ko shaida dalilan da suka sa ‘yan Najeriya suka sare da bada bayanan ba.

Related posts

Leave a Comment