Labarin dake shigo mana daga Jihar Bauchi na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga da ake zaton yan fashin daji ne sun kai kazamin hari ?aramar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi, ?aramar hukumar da Gwamna ya fito inda suka kashe mutum hudu, wasu uku suka jikkata.
Wasu majiyoyi daga yankin da suka ha?a da jami’an tsaro sun bayyana cewa lokacin da yan bindigan suka kai hari Tudun Wadan Jada, wanda mutane suka fi sani da Jimari Jauro-Bano da nufin sace mutane, an ankarar da mutane.
Matasan ?auyen da wasu daga kauyukan da ke kewaye suka ha?a kan su suka tunkari maharan, hakan ya sa yan bindigan suka gaza tafiya da mutane.
Amma da maharan suka ga ba zasu cimma kudirin su ba sai suka bu?e wa matasan wuta, nan take hudu suka mutu yayin da wasu uku suka ji munanan raunuka.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai da shara?in ?oye sunansa cewa: “Maharan sun shigo kauyen da misalin ?arfe 11:45 na daren ranar Alhamis, sun shigo a mashina, da mutane suka farga sai suka bu?e wuta, sannan suka tsere daji.
Bisa rashin sa’a mutum hu?u suka mutu, wasu uku suka jikkata.” Yace an gaggauta kai wa?anda suka jikkata wani Asibiti a jihar Gombe, jihar da take kusa da Bauchi.
Shugaban ?aramar hukumar, Yusuf Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin ga yan jarida ranar Jumu’a, inda ya ce maharan sun shiga sabuwar Tudun Wadan Jada da nufin sace mutane, da mutane suka farga sai suka tsere.
Ya ce yan bindiga sun shiga yankin ta dazukan dake da iyaka da Taraba, Gombe da Filato. Ya ?ara da cewa jami’an tsaro sun bazama domin kamo su. Garba ya ?ara da cewa sun gudanar da taron tsaro don tattauna lamarin da Sakataren gwamnati da shugabannin hukumomin tsaro yayin da aka jibge jami’ai a yankin.
Duk wani yunkurin jin ta bakin hukumar yan sanda ya ci tura kasancewar kakakin yan sandan Bauchi, SP Ahmad Wakil bai ?aga kiran waya ba.
