Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar wani yaro matashi dan shekaru 19 ya bayyana yanda ‘yan Bindiga da suka saceshi a Kaduna suka yanke masa hannu duk da biyansu kudin Fansa, Naira Miliyan 1.
‘Yan Bindigar sun saki Zakariya Iliya inda ya koma garinsu na Unguwan Gora a karamar hukumar Chukun ake masa maganin gargajiya.
Matashin yace a ranar zaben shugaban kasa da ya gabata ne ‘yan Bindigar suka saceshi da wasu mutane 5.
Yace sai da iyayensa suka sha fama kamin su samu kudin da suka biya aka sakeshi na Miliyan 1.
