Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘yan bindigar da suka yi fashin jirgin kasan Abuja-Kaduna wa?anda ake zargin ‘yan ta’addan ?ungiyar Ansaru ne sun sako wata fasinja mai juna biyu.
A cikin wani faifan bidiyo da Daily Nigerian ta samu, matar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tattauna da ‘yan ta’addan domin ceto rayukan sauran wa?anda ke hannu.
Ta ce wadanda suka yi garkuwa da su na kula da su, suna ciyar da su da kyau har ma da ba su magunguna. An ruwaito daga majiyar tsaro cewa ba a biya kudin fansa ba domin a sako ta, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Majiyar ta kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa wata mata ta haihu a hannun ‘yan ta’addan inda aka bayyana labarin a matsayin mara tushe ballantana makama.
Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin ceto fasinjoji sama da 60 da aka yi garkuwa da su a ranar 28 ga Maris, 2022, amma har yanzu yawancinsu suna hannu.
An bayar da rahoton cewa an sako mutum biyu bayan makudan kudin fansa. Wadanda aka sako – Manajan Daraktan Bankin Noma, Alwan Hassan da dan kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi.
