Fitacciyar jarumar Kannywood Aisha Aliyu Muhammad (Tsamiya) ta yi garga?in cewa akwai wasu masu amfani da sunan ta a manhajar Facebook su na zambatar mutane.
Jarumar ta ce akwai masu amfani da sunan ta su na tallata kayan da ta ke ?orawa a shafin ta na Instagram domin damfarar mutane.
Tsamiya, wadda ta yi wannan garga?in a wani guntun bidiyo da ta fitar a daren jiya, ta ce ita sam ba ta amfani da Facebook.
A cewar ta, duk shafin da aka gani da sunan ta a Facebook, to na bogi ne.
Haka kuma ta ja hankalin abokan hul?ar ta da su kula da wa?anda za su tura wa ku?i a duk lokacin da su ke da bu?atar kasuwanci da ita.Aisha Tsamiya na yin bayani a cikin bidiyon da ta tura a yau
A sa?on bidiyon da ta fitar na tsawon minti biyu, Tsamiya ta ?ara da cewa, ”Ha?i?anin gaskiya ni ban ta?a bu?e ‘account’ da suna na a Facebook ba, duk ‘account’ da kuma ‘pages’ da su ke a Facebook duk na ?arya ne, ban san shi ba kuma ba ni da ala?a da shi.”
Ta ce, ”Kwana biyu akwai abubuwan da su ke faruwa idan na yi ‘posting’ ?in kayayyakin da na ke sayarwa a Instagram, mutane da su ke amfani da suna na a shafin Facebook su kan yi ‘screenshot’ su ?ora kuma mutane su kan tura masu ku?i, don haka duk wanda ya san zai sayi kaya na, ya saya ta Facebook to kar ya ?auka cewa a guri na ya saya, ba ni da ala?a da wannan. Don haka jama’a don Allah a kiyaye. Ni ba na Facebook, ba ni kuma da wata ala?a da duk wani ‘page’ da ke Facebook.”
Kazalika ta ?ara da cewa, ”’Account number’ da su ka tura wa mutane GT Bank ne wanda ni kuma ‘account’ ?in da ake tura mani ku?i na bizines ?i na na ‘Zenith Bank’ ne.
”In dai ba Instagram ?in mu mutum ya bi na ‘Aisha Beauty Palace’ ba, ko kuma ‘WhatsApp number’ da na ke sawa a duk lokacin da na yi ‘posting’, don haka bayan nan babu wani. Kar wani ya tura ku?in sa ya zo ya na gaya min cewa ‘na sai kaya ta Facebook na tura miki ku?i an damfare ni ko an cuce ni.’ Idan ka tura ba ni ka tura wa ba. A kiyaye.”
