Labarin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewar an binne Gawar Deborah Samuel, dalibar kwalejin ilmin Shehu Shagari da aka kashe a jihar Sokoto kan laifin kalaman batancin ga Manzon Allah.
An ruwaito cewa an binne Deborah ne a mahaifarta, Tungar Magajiya, dake karamar hukumar Rijau a jihar ta Neja.
An binneta da misalin karfe 6:30 na yammacin jiya a makabartar Kirista dake Tunga Magajiya a yankin ?aramar hukumar Rijau dake jihar ta Neja.
Da farko matasan garin Tunga Magajiya sun ki amincewa a binneta inda suka ce gwamnatin jihar Sokoto ya kamata su dau nauyin jana’izar. Amma babba yayanta wanda Fasto ne a cocin ECWA< Emmanuel Maaji, ya jagoranci bizneta.
