Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ‘yan Bindigar da suka sace mutane 60 a cocin Emmanuel Baptist dake Kakau Daji, karamar hukumar Chikun, sun harbe mutum 2 har lahira.
A kwanakin baya ne ‘yan bindigan suka kai farmaki babban cocin suka kashe mutum ?aya, kuma suka sace wasu.
Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Jumu’a, ?arayin suka bukaci a kai musu buhunan shinkafa, jarkokin man gya?a, wanda a cewarsu zasu yi amfani da su wajen ciyar da mutanen.
Sha’anin tsaro dai na cigaba da samun matsala a jihar Kaduna, tun bayan matakin da Gwamnan jihar Nasiru El Rufa’i ya dauka na kin yadda da sulhu da ‘yan Bindiga, matakin dake shan yabo da suka daga jama’a.
