Filato: Shugabannin APC Sun Jaddada Goyon Bayan Lalong Kan Takarar Shugabancin Kasa

Shugabannin jam’iyyar APC na jihar Filato sun kare kudirinsu na mara wa gwamnan Jihar Samuel Lalong baya ya nemi kujerar Shugabancin Najeriya a za?en 2023 dake tafe.

Yayin ganawarsu a Jos babban birnin Jihar ranar Lahadi domin tattauna kudirin mara wa Lalonga baya, Shugabannin sun kuma tattauna kan rikicin dake wakana a majalisar dokokin jihar.

A taron nasu, shugabannin sun bayyana cewa Lalong yasan hanyoyin shawo kan matsalolin siyasa, hakan yasa rikicin majilisar bai yi muni ba.

Da yake zantawa da manema labarai a madadin shugabannin jim ka?an bayan taronsu, Saleh Mandung Zazzaga, yace gwamna Lalong zai ?aga martabar ?asar nan zuwa inda mutane basa tsammani shi yasa suke rokonshi ya amince ya fito takarar.

A cewarsa sun yi wannan hasashen ne duba da nasarorin da ya samu na rikice-rikice da kuma yadda ya saita sabanin da ake samu na banbancin ?abila ko addini a jihar Fitalo.

Ya ?ara da cewa duk da rikicin da ake samu nan da can, gwamnan bai yi ?asa a guiwa ba wajen jawo kowane bangare a cikin gwamnatinsa. Yace: “Lalong ne yake jagorantar ?ungiyar gwamnonin Arewa, kuma mafi yawan mutanen wannan yanki da ma na waje na yaba wa da tsarin mulkinsa.”

Lalong yana da kwarewar da Najeriya ke bukata Zazzaga ya kara da cewa gwamna Lalong yana da duk wata kwarewar siyasa wajen ?aukaka Najeriya zuwa babban matsayi da kuma ?ara dankon ha?in kai.

Related posts

Leave a Comment