Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya ce birnin Zariya na cikin tsaka mai wuya.
Sarkin ya bayyana hakan ne a yau Litinin lokacin da ya kar?i ba?uncin tawagar Shugabannin Tsaro ?ar?ashin jagorancin Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samueal Aruwan.
Sarkin ya ce mazauna bairnin ba sa samun barci da ido a rufe saboda sace-sacen mutane da ake yin don neman ku?in fansa a cikin birnin da kewayensa.
Ya bayyana yanayin a matsayin wanda ba za a amince da shi ba, tare da yin kira ga gwamnati da ta ?auki mataki, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Alhaji Bamalli ya ce duk da cewa akwai cibiyoyin tsaro kamar makarantar horar da sojoji a yankin masarautar tasa, amma al’ummarsa na zaune cikin fargaba.
Shi kuwa Kwamishina Aruwan cewa ya yi sun je fadar ne don ?ara ?warin gwiwa tare da jajanta wa masarautar kan harin da aka kai Makarantar Koyon Fasaha ta Nuhu Bamalli da kuma wasu al’ummomin ma?wabta.
Ya ce gwamnati na yin bakin ?o?arinta don kare masarautar da jihar baki ?aya.
