2023: Kuyi Watsi Da Batun Addini Da Kabila Ku Zabi Cancanta – Sanusi

Khalifan Tijjaniyya na Najeriya Muhammadu Sanusi II, ya bu?aci wadanda suka cancanci ka?a ?uri’a su je su yanki katin za?e gabanin babban zaben 2023.

Yana magana ne a wajen taron shekara-shekara na tunawa da ranar haihuwar mazon Allah Annabi Muhammad SAW a garin Lokoja.

Sanusi ya yi kira ga jama’a idan za?en ya zo su za?i shugabanni na gari ba tare da la’akari da siyasa ko addini ba.

“Idan matasanmu suka samu aikin yi, tattalin arzikin kasar baki daya zai inganta. Mafi mahimmanci, mu ba jam’iyya ba ce, amma ba za mu iya na?e hannayenmu mu yi watsi da siyasa ba” in ji shi.

“Duk dan Tijjaniyya daga shekara 18 zuwa sama namiji ko mace je ka karbi katin zabe. Allah yana umurce ku da ku dogara ga hannun muminai amintattu.

Yanzu muna wani lokaci da jama’a ne ke da ikon na?a shugabanni, ?uri’arku ita ce ?arfin ku, kuna da nauyi a kanku’’ a cewar Muhammadu Sanusi II.

Related posts

Leave a Comment