Da Dumi-Dumi: Bam Ya Tarwatse A Kaduna

Rahotannin dake shigo mana yanzu daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Kakakin rundunar ?an sandan Jihar Mohammed Jalige ya tabbatar da fashewar bam a unguwar Kabala West dake cikin garin Kaduna.

Jalige ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya NAN cewa babu wanda ya rasa ransa ko kuma rauni a fashewar bam din.

” Babu wanda ya ji rauni ko kuma rasa rai. A lokacin da bam din ya fashe babu kowa a gidan. Zuwa yanzu mun tattara sauran abin da ya fashe din kwararru na dubawa domin sanin ainihin abinda ya fashe.

Jalige ya ce rundunar zata bada karin bayani nan gaba.

Related posts

Leave a Comment