Yajin Aikin Kaduna: Sulhu Ne Alkhairi – Jakadan Hayin Banki

An bayyana cewa hawa teburin shawara shine mafita dangane da halin da Jihar Kaduna ta tsinci kanta yanzu a ciki na ta?addama tsakanin Gwamnan Jihar Kaduna da kungiyar ?wadago ta kasa lamarin da ya sabbaba shiga cikin yajin aikin da talakawa ke ji a jikin su.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani jigo a jam’iyyar APC ta Jihar Kaduna mai suna Alhaji Abdullahi Gambo Abba lokacin da yake tsokaci dangane da yajin aikin da ke gudana yanzu haka a Jihar ta Kaduna.

Gambo Abba wanda ke rike da sarautar Jakadan Hayin Banki Kaduna ya cigaba da cewar, zama teburin shawara tsakanin bangarorin biyu na da matukar fa’ida domin shi zai taimaka wajen lalubo bakin zaren da magance matsalar ba tare da cutar da sauran jama’a ba.

“Domin a halin da ake ciki yanzu babu masu shan wahala dalilin wannan yajin aikin sai jama’ar Jihar, wa?anda yajin aikin ya jefasu cikin matsananciyar damuwa.

Daga ?arshe ?an siyasar ya yi addu’a gami da fatan Allah daidaita tsakanin kungiyar ?wadagon da gwamnatin Jihar, domin abubuwa su dawo bisa ga tsari.

Related posts

Leave a Comment