Masari Ya Roki Katsinawa Su Taimaka Wajen Samar Da Tsaro A Jihar

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamnan jihar Alhaji Aminu Bello Masari, ya bukaci kafatanin jama’ar Jihar da su bada tasu gudummuwar wajen ganin tsaro ya dawo Jihar kamar yadda aka san ta a baya.

Gwamna Masari, ya bayyana haka ne yayin da ya kar?i ba?uncin wakilan ma’aikatan jihar wanda babban al?alin jihar, Justice Abubakar Musa ?anladi, ya jagoranta domin yi masa Barka da sallah a gidan gwamnati.

Masari yace gwamnatinsa tana gudanar da al’amuran mulki kamar yadda kundin tsarin mulkin ?asa ya tanadar kuma tana baiwa duka ?angarorin gwamnati uku damar gudanar da ayyukansu.

Gwamnan yace: “Gwamnatin mu ta rungumi masu rike da mukaman siyasa da kuma ma’aikata daban-daban na jihar da zuciya ?aya, domin amfanin al’ummar mu, bawai don mu burge wasu tsirarun mutane ba.”

“Nayi iya bakin ?o?arina ganin na baiwa masu ri?e da manyan ofisoshi damar yin aiki ?ar?ashin doka, hakanan na bar kofa ta a bu?e garesu, domin dawo da aminci da yarda da juna.”

“Tun daga lokacin da na shiga ofishin gwamnan jihar nan, na fara shiryawa zuwan ranar da zan fita, ina fatan zan sauka cikin aminci idan lokacina ya ?are.”

Gwamnan yayi kira ga jama’ar jihar da su taimaka wa gwamnatinsa a ?o?arin da take na magance matsalar tsaro, farfa?o da tattalin arzi?i da kuma ?alubalen ?angaren lafiya.

Shugaban wakilan ma’aikatan gwamnati, Justice Abubakar, yace sun zo ne suyi wa gwamnan barka da Sallah da kuma fatan akairi. Yace zasu cigaba da baiwa gwamnan goyon baya domin kawo cigaba a fa?in jihar.

Related posts

Leave a Comment