Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya sake kafa wani kwamiti don sake duba bukatun kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU
Kungiyar ta tsunduma yajin aiki ne a watan Fabrairu saboda wasu bukatu da suka hadar da inganta jami’o’in kasar, da sabon tsarin biyan malaman jami’a na UTAS, da sauran wasu bukatu.
Tuni dai gwamnatin tarayya ta daina biyan malaman albashi, tana mai cewa bai kamata a biya su ba tunda ba su yi aiki ba, kuma ba za a biya su watannin da suka shafe suna yajin aikin ba.
Matakin ya kara harzuka malaman jami’ar.
To amma a zaman da gwamnatin kasar ta yi da iyaye da shugabannin jami’o’i mallakar gwamnatin tarayya ranar Talata, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya ce gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti domin sake duba batun.
Malam Adamu Adamu ya ce kwamitin zai kunshi iyayen jami’o’i hudu, da shugabannin jami’o’i hudu a yayin da shi kuma zai jagoranci kwamitin.
