Rahoton dake shigo mana daga Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa na bayyana cewa domin ganin an magance matsalar canjin yanayi ne yasa aka shirya wa manoma da malaman gona taron kara wa juna sani na kwana daya, a Jami’ar Modibbo Adama dake Yola.
Cibiyar kimiyyar kasa ta Najeriya tare da hadin gwiwar jihohin Adamawa da Taraba ne suka shirya taron wanda aka gudanar a tsangayar karantar da harkokin gona na Jami’ar Modibbo Adama dake Yola.
Da yake jawabi a wurin bude taron mataimakin Shugaban Jami’ar Farfesa Ŕbdullahi Liman Tukur kira yayi wa Manoma da malaman da su kasance masu mai da hankali wajen irin matsalar da ake fuskanta na canjin yanayi domin ganin an kawo karshen matsalar baki daya.
Ya kuma yaba da yadda aka dauki matakin na wayar wa Manoma kai dangane da matsalar na canjin yanayi.
Da yake gabatar da lakca akan matsalar canjin yanayi Dr Hassan Musa yace canjin yanayi yana iya faruwa a kowane lokaci don haka akwai bukatar a maida hankali wajen magance matsalar baki daya.
Ya kuma kirayi mahalarta taron musammanma malaman gona da suyi amfani da abinda aka koya musu ta fadadawa zuwa ga manoma dake yankunansu, wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen magance matsalar baki daya.
