?angaren Gwamnatin Tarayya za su yi zama da Kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU a yau Juma’a, 20 ga watan Nuwamba, 2020, da nufin ganin karshen yajin-aikin da Kungiyar ta lashe watanni da dama tana yi.
Mataimakin Daraktan yada labarai na ma’aikatar kwadago, Charles Akpan, ya bada sanarwar wannan zama da gwamnati za ta yi da malaman jami’a a babban birnin tarayya Abuja.
Kamar yadda Mista Charles Akpan ya bayyana, za ayi zaman ne da karfe 11:00 a dakin taron ma’aikatar. Bangaren gwamnati bai yi karin-haske game da batutuwan da za a tattauna game da su ba, amma ana sa ran cewa ayi kokarin ganin an bude makarantu.
Chris Ngige da sauran wakilan gwamnatin tarayya za su yi bakin kokarinsu na ganin ASUU ta janye dogon yajin-aikin da ta shafe wata da watanni ta na yi.
A zaman da aka yi na karshe, gwamnati ta fada wa malaman jami’ar cewa ba ta da kudin da su ke sa ran za su samu bayan alawus dinsu.
Ministan kwadago, Ngige ya nuna cewa abin da za su iya ba ASUU ba zai zarce Naira biliyan 40 ba, sai kuma Naira biliyan 20 na gyaran jami’o’in kasar.
A halin yanzu kungiyar ta fara koka wa game da yadda tattaunawarsu da gwamnati ya ke daukar lokaci, malaman sun zargi gwamnati da yaudarar jama’a.
Kwanakin baya kun ji yadda Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga Malaman Jami’a su rungumi noma, wannan maganar ba ta yi wa kungiyar ASUU dadi ba. Ministan ilmi ya ce gwamnati ba ta rike malaman jami’a ba, don haka za su iya ajiye aikinsu.
