Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ‘yan sanda Najeriya Usman Baba ya bayyana cewa mayakan Boko Haram na kista shirin kai hari a Birnin Abuja da Jos a jihar plateau, abinda yasa kwamishishonin ‘yan sanda wadannan yankuna cikin ko ta kwana
Baba ya ce bayanan sirri da suka samu ya nuna musu cewar bangaren boko haram dake karkashin Muhammad Sani dake da cibiya a Sambisa da kuma mataimakin sa Suleiman dake Jihar Yobe ke shirya kai harin.
Bayan gargadin jami’an ‘yan Sandan dake wadannan yankuna wajen ganin sun zauna cikin shirin ko ta kwana, Sufeto Janar din ya kuma bukaci mazauna yankunan su dinga sanya ido kan abinda ke faruwa kusa da su wajen kai rahoto ga jami’an tsaro kan abinda basu gamsu da shi ba.
Wannan mataki na zuwa ne makwanni bayan da gwamnan jihar Niger Sani Bello ya bayyana cewar birnin Abuja na cikin hadari ganin yadda suka mamaye wani yanki na jihar sa.
