Labarin dake shigo mana daga Makurdi babban birnin jihar Binuwai na bayyana cewar Gwamna Samuel Ortom na jihar a ranar Juma’a, ya bayyana godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da majalisar kolin kasa bisa afuwar da suka yi wa tsaffin gwamnonin jihohin Filato da Taraba, Sanata Joshua Dariye da Rabaran Jolly Nyame.
Dariye da Nyame dai na zaman gidan kaso ne a gidan yari a Kuje da ke Abuja, biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke musu kan badakalar kudi a lokacin da suke gwamnoni tsakanin 1999 zuwa 2007.
A yayin da Ortom ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na ARISE makwanni biyu da suka gabata, ya roki gwamnatin tarayya da ta sake duba shari’ar Dariye da Nyame, da nufin yi musu afuwa.
A ranar Alhamis ne Majalisar Kolin karkashin jagorancin Buhari ta yi taro a Abuja inda rahotanni suka ce sun yi la’akari da yin afuwa ga Dariye, Nyame da sauran wadanda ke zaman gidan kaso.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Ortom, Nathaniel Ikyur ya fitar, ya ce gwamnan ya godewa shugaba Buhari da majalisa da kuma gwamnatin tarayya bisa wannan matakin duk da cewa ya yarda cewa lallai an koyi darassu masu amfani daga lamarin.
