Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar Shugaban ?asa ta yi watsi da kiraye-kirayen da ?ungiyar Dattawan Arewa ta yi, inda ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki, saboda kasa magance matsalar tsaron ?asar nan.
Fadar ta ce ana kan fito da wani gagarimin tsarin tsaurara tsaro a fa?in ?asar nan, nan ba da da?ewa ba.
Wannan bayani na cikin wata sanarwa da Kakakin Ya?a Labaran Shugaba Buhari, Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba.
Shehu ya ce murabus ?in shugaban ?asa ba shi ne mafita ba ga matsalar tsaron da ake fama da ita.
Ya ce tuni jami’an tsaro sun ?ara ?aimi wajen da?ile ‘yan ta’adda, musamman a Jihar Kaduna da Neja da kuma yankin Neja Delta, kamar dai yadda Shugaban ?asa ya umarce su.
Garba ya ce ?angarorin tsaro sun ha?a kai wajen ci gaba da farmakin yin galaba a kan masu haddasa matsalar tsaro, kuma ana ganin alamun nasara.
“Fadar Shugaban ?asa ba ta so ta na biye wa masu neman jan ta ana hauragiyar cika kafafen ya?a labarai da maganganu, kamar yadda Kungiyar Dattawan Arewa ta yi, wato NEF
“Son neman a sani aiki ne na ‘yan siyasar da ba su ka kasa samun yardar talakawa masu za?e.
“Ya isa ta ?angaren mu, mu fito mu ce murabus ?in Shugaban ?asa a yanzu ba shi ne mafita daga matsalar tsaron da ?asar nan ke fuskanta ba.
“A sani wannan matsala ce fa da ta da?e shekara da shekaru ana fama da ita, daga nan kuma wannan gwamnatin ta gaje ta, bayan gwamnatocin baya sun yi watsi da ?o?arin da?ile ta.
“Ya na da muhimmanci ?warai jama’a su san irin ?o?arin da wannan gwamnatin ke yi, wajen ganin ta magance matsalar tsaro.
“Su kuma ‘yan siyasa ya na da kyau su sani kamata ya yi su taimaka ?asa ta ?ore, ta yadda idan lokacin su ya yi, su ma su sami wurin da za su yi wa mulki.
“Saboda idon mutum ya rufe da neman mulki, bai kamata ya tarwatsa ?asar ya ke son ya ?are kan mulkin ta ba.
“Ma’aikatar Tsaro na bakin ?o?arin ta wajen ganin cikin gaggawa kwanan nan ta fito da tsare-tsare da kuma kai farmaki a yankunan Kaduna da Neja, kamar yadda Shugaba ?asa ya ba su umarni.
“A wurin Taron Majalisar Zartaswa na ranar Taraba, an amince a sayo tulin makaman da ba a ta?a a ta?a kawo masu yawan su ba a lokaci guda.”
Ya ce a yanzu haka ana samun gagarimar nasara, ana kama ?imbin masu hana ?asar nan.
Ya ce gwamnatin tarayya za ta cika al?awarin ta na samar da dawwamammen zaman lafiya a fa?in Najeriya.
