Tsohon shugaban kwamitin kwararru da aka kafa domin bincike da kwato kudin jama’a da aka sace, Okoi Obono-Obla ya fadi inda aka kai kudaden. Mista Obono-Obla ya yi ikirarin cewa dukkanin kudin da aka kwato a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari an mayar da su ga barayin kasar ne.
Ya kara da cewa gwamnatin Buhari ta gaza a wajen yaki da cin hanci da rashawa, gwamnatin da ya ce al’ummar Najeriya suka dorawa yarda in ji rahoton
Obono-Obla, wanda Buhari ya nada shi matsayin hadiminsa, ya yi wannan ikirarin ne a ranar Asabar a yayin tattauna da wata kafar labarai, Mic On Podcast.
A cewar Obono-Obla, kokarin da ya yi na ganin an gurfanar da masu wawure dukiyar kasa a gaban kotu, ya samu nakasu daga wasu jami’an gwamnatin Buhari.
Tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan tarayya, Abubakar Malami, wanda shi (Obono-Obla) ya bayyana a matsayin ‘mai mulki’ na daga cikin wadanda suka kawo tsaikon.
Badakalar shigo da motocin sulke 80 Obono-Obla ya ce: “Wasu daga cikin abubuwan da na kwato an mayar da su ga barayin. Misali, akwai wani lokacin da na kwato sababbin motocin X-class Mercedes Benz (masu sulke) sama da 80 a Jabi, Abuja hannu wani mutumi.
“Na tuntubi hukumar kwastam da hukumar shige da fice kan ko suna da masaniyar shigo da motocin, suka ce ‘a’a’, amma Malami ya hana ni daukar mataki akai, wai bai aike ni ba.”
Badakalar sanata mai boye kudi a waje Obono-Obla ya ci gaba da cewa:
Akwai kuma batun wani sanata wanda a lokacin yana kan kujerar sa kuma daga baya ya zama shugaban majalisar dattawa, shi ma na ci karo da badakalar da ya tafka. “Na sami bayanan a cikin takardun Panama, wanda ya bayyana cewa yana da dukiya a kasashen waje, Ba ni da hurumin bincikensa saboda kudin na kasar waje.
“A lokacin na nemi taimakon shugaban hukumar NIA, wanda ya tabbatar mun da zargina, amma Malami ya hana ni daukar mataki akai, har yanzu ba a kara tado da maganar ba.”
