Wata sabuwar batarna?a ta kunko kai a Kano, yayin da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir-Yusif ya sha alwashin ?wato ku?a?en fansho N5.4bn da gwamnatin tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ba ta biya ba, amma kuma ta fitar da ku?a?en.
Gwamna Abba Kabir-Yusuf na Jihar Kano ya ce a shirye ya ke ya yi amfani da duk wata hanya ta doka wajen kar?o ku?a?en fansho da Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ke cirewa duk wata daga albashin ma’aikata da suka kai sama da Naira biliyan 5 kuma ba a sanya su a asusun gwamnati ba.
Gwamnan ya ce ba za a amince da wani ya cire ku?a?en fansho na ma’aikata duk wata ba, kuma ba tare da an tura ku?a?en ba.
Da yake Jawabi a lokacin bikin bayar da garatuti Naira biliyan 5 ga ma’aikata 4,000 da suka yi ritaya, Gwamna Abba ya lura cewa biyan fansho ba gata ba ne ga ma’aikata face ha??in su ne da ya wajaba a biya su.
Gwamnan ya bu?aci ‘yan fanshon da su rubuta takardar koke ga Gwamnatin Jihar Kano, domin a binciki yadda ake cire musu ku?a?en fansho duk wata.
Ya ba da tabbacin cewa gwamnatin sa za ta tabbatar an ?wato musu ku?a?en su.
Ya ci gaba da cewa, “abbatarwar da muke muku yanzu ita ce, duk ku?a?en da aka cire daga cikin ku?a?en fansho a duk wata da suka haura Naira biliyan 5 ba a tura su a baitul malin gwamnati ba, sai dai muna zargin an kai su a wani asusu na sirri ne, amma mun ?udiri aniyar ?wato su ta hanyar doka”, gwamnan ya tabbatar da haka.
Gwamna Abba ya ?ara da cewa gwamnatin sa ta gaji bashin Naira biliyan 43 na fansho daga gwamnatin Ganduje.
Abdulkadir Abdussalam Babban Akanta Janar na Jihar Kano, ya bayyana cewa Gwamna Yusuf ya ?udiri aniyar biyan ku?a?en fansho na shekaru goma.
Shugaban Kungiyar ’Yan fansho ta Najeriya reshen Jihar Kano, Kwamared Salisu Gwale ya bayyana cewa kafin za?en 2023, “mun tambayi yadda sabuwar gwamnati za ta magance matsalar ‘yan fansho a Kano da sama da Naira biliyan 43 da ba a biya ba.
Salisu Gwale ya nuna ba?in cikin sa kan yadda gwamnatin Ganduje ta yi
wa harkar fansho ri?on sakainar kashi.
