Hukumar kula da kafafen ya?a labaru ta ?asa NBC ta ci tarar kafar ya?a labaru ta Arise saboda zargin ta da ya?a labarin ?arya.
A ?arshen makon da ya gabata ne Arise TV ya yi wani labari da ke cewa hukumar za?e na binciken ?an takarar shugaban ?asa na jam’iyyar APC, Tinubu, bisa dogaro da wani labarin da aka rin?a ya?awa a shafukan intanet.
NBC ta ce abin da kafar Arise ta yi, “gagarumin karan-tsaye ne ga dokar ya?a labaru ta ?asa sashe na 5.1.3, da rashin iya aiki, da kuma rashin tunani a wannan lokaci da ake ya?in neman za?e.”
Saboda haka sanarwar wadda ta samu sa hannun shugaban hukumar, Balarabe Shehu Illela, ta bu?aci Arise TV ya biya tarar naira miliyan biyu a cikin wa’adin mako biyu.
A ranar Lahadi ne dai kafar Talabijin ?in na Arise ya nemi afuwar ?an takarar shugaban kasa na jam’iyyar A.P.C, bayan da hukumar za?e mai zaman kanta ta fitar da wani bayani kan cewar labarin da ake ya?awa da ke cewa tana bincike kan Bola Tinibu ba gaskiya ba ne.
Hukumar ta NBC ta kuma bu?aci kakafen ya?a labaru da su rin?a tantance duk wani labari da suka samu gabanin wallafa shi, musamman ma wanda aka samu a shafukan sada zumunta.
