Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa lokaci ya yi da ?an Najeriya za su ha?u guri guda domin su ya?i makiyan al’ummar Najeriya.
Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a cikin sa?on ta’aziyyar kisan da wasu ?an bindiga su ka yi wa ?an Najeriya a wasu ?auyuka da ke ?aramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.
“Na kadu matuka da samun labarin kisan gillar da aka yiwa ‘yan Najeriya sama da sittin a kauyukan Kadawa da Kwata, dake Karamar Hukumar Mulkin Zurmi, a Jihar Zamfara, tabbas abin kyama ne tare da Allah-wadai, domin wannan zunzurutun zalunci da babu wani mai hankalin da zai amince da shi”
“Cikin yanayi na alhini, Ina mika sakon ta’aziyyata da jaje ga Gwamnati da al’ummar jihar Zamfara bisa wannan mummunan hari”
“Hakaki lokaci ya yi da zamu dunkule wuri daya mu tunkari makiyan kasar mu da al’ummar ta, domin suna barazana ga ci gaba da kasancewar mu masu zama a cikin ta”
Atiku ya ?ara da cewa “Lokaci ya yi da zamu fahimci cewar sha’anin kula da tsaro bai tsaya kadai kan hukumomi ba, a’ a muma ‘yan kasa muna da gudummawar bayarwa wajen tunkarar wannan matsala”
A karshe Atiku ya ce “Amma ina ?ara kira ga hukumomin tsaron da su kara mikewa tsaye domin tunkarar wannan babbar barazana”
