Ya Kamata Masu Zanga-Zangar SARS Su Dakata Haka – Shugabannin Majalisa

Shugaban majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya yi kira ga masu zanga-zangar neman kawo karshen rundunar SARS a fadin Najeriya da su yi hakuri su dakatar da zanga-zangar a haka.

Lawan ya bayyana hakan ne bayan ganawar da ya gudana tsakaninsa da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da kuma kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.
Sun yi ganawar ne a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Lawan ya jadadda cewa ya kamata masu zanga-zangar su janye tunda sun gabatar da kokensu kuma gwamnati ta dauki mataki kan haka.

Ya kara da cewa wannan zanga-zanga da ake yi yana takura wa al’umma musamman masu gudanar da harkokin kasuwancinsu. Tunda gwamnati ta amsa kokenku lokaci ya yi da ya kamata a daina wannan zanga-zanga.

“Tun da gwamnati ta amince da bukatun da masu zanga-zangar suka gabatar mata, lokaci ya yi da masu zanga-zangar za su daina, gwamnati na bukatar lokaci domin aiwatar da bukatun masu zanga-zangar,” in ji Lawan.

A nashi bangaren, kakakin majalisar wakilai, Gbajabiamila ya yi kira ga kawo karshen zanga-zangar, inda ya bayyana cewa ba za a iya aiwatar da manufa a dare daya ba.

Ya kuma jinjinawa masu sanya-zangar a kan namijin kokarin da suka yi, ya basu tabbacin cewa suna iya ci gaba da zanga-zangar idan ba a cika masu bukatunsu ba a makonni biyu.

Related posts

Leave a Comment